Mr. Yan Wang, ya ce Sin na da burin daga matsayin wannan alaka da daukacin kasashen dake nahiyar Afirka, wadda ita ce nahiya ta biyu mafi girma a dukkan fadin duniya.
Ya ce a shekarar 2013 bisa tallafin babban bankin duniya, Sin da sauran kasashe masu samun ci gaba, suka kaddamar da wani shiri mai lakabin PASET, domin raya harkokin kimiyya da fasaha, da kirkire kirkire a nahiyar Afirka. (Saminu)