in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan harkokin wajen kasar Sin ya halarci taron ministocin harkokin wajen kasashe mambobin SCO
2017-04-21 20:41:16 cri

Yau Jumma'a ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya halarci taron ministocin harkokin wajen kasashe mambobin kungiyar hadin gwiwar Shanghai wato SCO a birnin Astana, hedkwatar kasar Kazakhstan.

A jawabin da ya gabatar yayin taron, Wang Yi ya ce, kasar Sin za ta zama jagorar kungiyar a zagaye na gaba, bayan taron kolin kungiyar wanda za a gudanar a watan Yunin bana, kuma Sin din ta fahimci babban nauyin da aka dora mata. Don haka take sa ran cewa, sassa daban daban za su ba ta shawarwari masu ma'ana.

Har wa yau Sin na fatan hada kai da sassa daban daban, a fannonin aiwatar da ra'ayi daya da shugabanni suka cimma, da raya kungiyar yadda ya kamata, a kokarin kara kawo wa jama'ar yankin alheri. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China