in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan Sin ya gabatar da shawarar kafa dandalin hadin gwiwa a fannoni 6 tsakanin mambobin kasashen kungiyar SCO
2015-12-15 15:43:25 cri
A ranar talata 15 ga wata, a birnin Zhengzhou da ke kasar Sin, yayin da firaministan Sin Li Keqiang ya halarci taron kwamitin firaministocin mambobin kasashen kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai wato SCO karo na 14 ne, ya gabatar da shawarar kafa dandalin hadin gwiwa a fannoni 6, a karkashin tushen tsaro, tattalin arziki da al'adu, don yalwata hadin gwiwa ta sada zumunta tsakanin bangarorin da abun ya shafa.

Wadannan fannoni 6 sun hada da, a kafa dandalin hadin gwiwa game da harkokin tsaro, da kafa dandalin hadin gwiwa game da makamashi, da kafa dandalin hadin gwiwar mu'amala da juna, da kafa dandalin hadin gwiwa a fannin hada-hadar kudi, da kafa dandalin hadin gwiwa kan cinikayyar shiyya-shiyya, da kafa dandalin hadin gwiwar raya zaman rayuwar al'umma.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China