in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya gana da shugabannin kasashe membobin kungiyar SCO
2015-12-16 14:46:32 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da shugabannin kasashe membobin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai wato SCO da suka hada da firaministan kasar Kazakhstan Karim Massimov, da firaministan kasar Kyrgyzstan Temir Sariev, da firaministan kasar Rasha Dmitry Medvejev,。

A lokacin ganawar tasu Mr Xi Jinping ya bayyana cewa, a matsayinta na wani muhimmin tsarin hadin kai na kasa da kasa a yankin Turai da Asiya, kungiyar SCO ta taka muhimmiyar rawa wajen kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali da kuma inganta bunkasuwar kasashe membobinta. A halin yanzu, yanayin duniya da tattalin arzikin kasa da kasa na samun sauyawa cikin sauri, shi ya sa, ya kamata kasashe daban daban su yi hadin gwiwa, don su samu bunkasuwa mai dorewa.

Bugu da kari, Xi Jinping ya jaddada cewa, kungiyar SCO na da tsarin hadin gwiwa mai kyau, kuma tana da makoma mai kyau wajen yin hadin gwiwa a tsakanin kasashe membobinta. Kasar Sin tana son yi kokarin tare da bangarori daban daban wajen raya kungiyar don kara ba da gundummawa kan tabbatar da zaman lafiya da bunkasuwar shiyyar.

A wajen taron, sauran shugabannin kasashen kungiyar ta SCO sun bayyana cewa, an cimma nasarar yin taron firaministoci karo na 14 na kungiyar. Don haka ya kamata kasashe membobi su yi amfani da wannan zarafi don karfafa hadin gwiwarsu a fannonin tattalin arziki da ciniki da hada-hadar kudi da zirga-zirga da kiwon lafiya da tarbiyya da kuma fasahohin yanar gizo.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China