Kwamitin kare al'adun gargajiya da ba na kayayyaki ba na kasa da kasa ne ya amince da wadannan alamomin a yayin zaman kwamitin karo na 11 karkashin kulawar hukumar kula da ilimi, kimiyya da al'adu ta MDD(UNESCO), taron da ya gudana daga ranar Litinin zuwa Jumma'a a birnin Addis Ababa na kasar Habasha.(Ibrahim)