Game da hakan, kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin Mista Lu Kang ya jaddada cewa, kasar Sin na adawa da duk wani mutum, wanda zai yi amfani da makamai masu guba bisa kowane dalili a kowane lokaci, kana hanyar siyasa, ita ce hanya daya tilo da za'a iya bi, wajen magance matsalar kasar.
A wajen taron manema labarai da aka yi a wannan rana, Mista Lu Kang ya ce, zaman tsintsiya madaurinki daya a tsakanin mambobin kwamitin sulhun MDD na da muhimmancin gaske, game da daidaita batun kasar Siriya.
Wannan dai daftarin kuduri game da Siriya, na kunshe da wasu abubuwan da kasar Sin ta amince da su, ciki har da yin tofin Allah tsine kan aika-aikar amfani da makamai masu guba a cikin Siriya, da bukatar yin bincike kan wannan batu. Amma akwai sauran wasu abubuwan da ya kamata a gyara su, kafin bangarori daban-daban su cimma matsaya.
Ya ce kasar Sin na nuna rashin jin dadinta bisa rashin cimma daidaito kan wannan kudiri a zaman kwamitin sulhun MDD. Wanda hakan ya san ya ta kauracewa jefa kuri'ar ta. (Murtala Zhang)