Wang ya ce, halin da ake ciki a Siriya na kara tabarbarewa, lamarin da ya kasance abun damuwa matuka. Wang ya bayyana matsayin gwamnatin kasar Sin a fannoni uku, wato da farko Sin na adawa da duk wani yunkuri na amfani da makamai masu guba, ta kuma yi tofin Allah tsine game da aikata hakan. Kaza lika Sin na goyon-bayan gudanar da bincike sosai kan amfani da makamai masu guba da aka yi a Siriya, ta yadda za'a kai fa fitar da sakamako bisa gaskiya. Kana, duk wani matakin da za'a dauka, ya zama wajibi a dauke shi karkashin jagorancin MDD, tare da bin ka'idojin kasa da kasa.
Ya ce abu na biyu, kamata ya yi a mutunta cikakken 'yancin kan kasar Siriya, gami da ikon mallakar kasar. Kuma al'ummar Siriya ya dace su warware matsalar kasarsu bisa radin kansu.
Na uku kuma Sin na ganin cewa hanyar siyasa, ita ce kadai da za'a iya bi domin kaiwa ga warware matsalar kasar ta Siriya. Kuma kasar Sin ta na fatan bangarorin dake da ruwa da tsaki, musamman Amurka da Rasha, za su inganta mu'amala tsakaninsu, domin kaucewa zaman ja-in-ja tsakaninsu. (Murtala Zhang)