in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta yi kira da a hana tabarbarewar halin da Syria ke ciki
2017-04-07 19:01:31 cri
A yau juma'a ne mai Magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying, ta bayyana cewa, abu mafi muhimmanci a yanzu haka shi ne hana tabarbarewar yanayin da kasar Syria ke ciki, don shawo kan matsalar siyasar kasar a siyasanci.

Hua wadda ke amsa tambayoyin da ake gabatar mata game da farmaki daga sama da sojojin Amurka suka kaddamar kan wani sansanin sojojin sama na kasar Syria yayin taron manema labaru da aka saba yi, ta kuma jaddada cewa, kasar Sin na tsayawa kan matsayinta game da batun makamai masu guba, inda take nuna rashin amincewa ga ko wace kasa, ko kungiya, ko mutum ya yi amfani da makamai masu guba bisa ko wane irin hali ko dalili. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China