Hua Chunying ta bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a wannan rana cewa, kamata ya yi jama'ar kasar Syria su tabbatar da makomar kasar su da kansu. Ta ce ya kamata kasashen duniya su girmama hanyar bunkasuwa da jama'ar kasar Syria suka zaba.
A hannu guda Sin na fatan ci gaba da kokari tare da bangarori daban daban na duniya, wajen sa kaimi ga warware batun Syria ta hanyar siyasa cikin hanzari.
Ban da haka kuma, Hua Chunying ta bayyana cewa, Sin na adawa ga duk wata kasa, ko kungiya, ko mutum, wanda ke amfani da makamai masu guba bisa ko wane irin yanayi. Kana tana goyon bayan MDD, a aikin ta na bincike kan zargin amfani da makamai masu guba, tare da gabatar da rahoto mafi dacewa da gaskiya. (Zainab)