in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Manzon musamman na Sin zai halarci shawarwarin shimfida zaman lafiya a Syria
2017-03-22 20:30:06 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying, ta bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a nan birnin Beijing a yau Laraba 22 ga watan nan cewa, manzon musamman na gwamnatin kasar Sin mai kula da batun Syria Xie Xiaoyan, zai halarci shawarwarin shimfida zaman lafiya a Syria karo na 5 a birnin Geneva, a wani mataki na ci gaba da gudanar da aikin shiga-tsakani, da ba da gudummawa wajen sa kaimi ga warware batun Syria ta hanyar siyasa.

Za a gudanar da shawarwarin shimfida zaman lafiya kan batun Syria zagaye na 5 a Geneva a ranar 23 ga watan nan, wannan ne kuma karon farko da gwamnatin kasar Syria, da wakilan kungiyoyin 'yan adawa za su yi shawarwari kan batun da suka amince da tattaunawa tare. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China