in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana fama da matsalar yunwa a Sudan ta Kudu, in ji hukumomin MDD
2017-02-20 19:28:50 cri

Rahotanni daga kasar Sudan ta Kudu na cewa, kimanin mutane 100,000 ne ke fama da matsalar yunwa a wasu sassan kasar sakamakon yaki da rugujewar tattalin arzikin kasar.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwar hadin gwiwa da hukumar abinci da aikin gona ta MDD(FAO) da asusun tallafawa yara na MDD(UNICEF) da shirin samar da binci na duniya(WFP) suka fitar a yau Litinin a birnin Juba, fadar mulkin kasar.

Hukumomin sun kuma yi kira da a hanzarta daukar matakan da suka wajaba, don ceto rayukan mutane kimanin miliyan biyar dake matukar bukatar abinci, aikin gona da kuma taimakon abinci mai gina jiki.

Sun kuma bayyana cewa, a halin yanzu ana fama da yunwa a wasu sassan jihar Unity dake arewa masu tsakiyar kasar, baya ga wasu karin mutane miliyan 1 da aka ayyana a matsayin wani rukuni da za su fada cikin matsalar yunwa.

Rahotanni na cewa, mutane sun fara mutuwa sakamakon matsalar yunwa, kuma wannan lamari shi ne mafi muni tun bayan da fada ya barke a kasar sama da shekaru uku da suka gabata.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China