Yayin taron manema labarai na kullum yaumin, Kakakin na MDD ya ce a karon farko, David Shearer ya kai ziyara garin Yambio dake yamacin yankin Equatoria, yankin da ya fi kowanne samun albarkatun gona, dake samar da kayayyakin abinci mai yawa ga sauran sassan kasar.
Dujarric ya ruwaito Mr Shearer na cewa, ayyukan gona sun ja baya saboda manoma basa noma, sanadaiyyar rikici da gudun hijira, yana mai cewa samar da tsaro na da mutukar muhimmanci wajen cinikayya da safarar kayayyakin gonan.
Hukumomin MDD sun ce tsakanin watannin Junairu da Maris din 2016, mutane miliyan 2.8 ne ke bukatar agajin gaggawa a kasar, kwatankwacin daya bisa hudu na al'ummar kasar, yayin da mutane dubu arba'in ke fuskantar yunwa. ( Fa'iza Mustapha)