Sanarwar ta ce, ba za a amince kan faruwar irin wannan lamarin ba a yayin da ake bukatar taimakon jin kai na gaggawa a kasar Sudan ta Kudu. Wannan ne kuma lamarin da aka fi samun rasuwar masu aikin ceto tun bayan afkuwar rikici a wannan kasa a watan Disamban shekarar 2013.
Game da hakan kuma, Owusu ya bayyana cewa, ba kawai wadannan lamuran kai farmaki sun kawo rasuwar masu aikin ceto ba ne, har ma sun kawo kalubale ga rayuwar 'yan kasar Sudan ta Kudu wadanda ke dogaro da samun taimako daga wajen masu aikin ceto na kasa da kasa.
Bisa kididdigar da sanarwar ta bayar, an nuna cewa, daga watan Disamban shekarar 2013 zuwa yanzu, a kalla masu aikin ceto 79 ne suka rasa rayukansu a sakamakon hare haren da aka kai musu. (Bilkisu)