Kasar Sudan ta Kudu na fama da tashe-tashen hankula a shekarun nan. A watan Afrilun shekara ta 2016, shugaban kasar wato Salva Kiir da madugun 'yan hamayyarsa wato Riek Machal, sun kafa gwamnatin hada kai ta rikon-kwarya, amma dakarun bangarorin biyu suka yi taho-mu-gama a watan Yulin bara, har Riek Machal ya tsere zuwa kasar waje. (Murtala Zhang)