Mataimakin wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Wu Haitao, ya ja hankalin kasashen duniya, da su yi duk mai yiwuwa wajen tabbatar da amfani da matakan siyasa, domin warware rikicin kasar Sudan ta Kudu.
Mr. Wu wanda ya yi wannan kira yayin taron kwamitin tsaron MDDr da aka gudanar domin tattauna halin da ake ciki a Sudan ta kudu, ya ce ya zama wajibi a ja hankalin sassan Sudan ta kudu, su dakatar da kai wa juna hari, su kuma koma teburin shawarwari, domin cimma yarjejeniyar wanzar da zaman lafiya mai dorewa.
Kaza lika Mr. Wu ya yi maraba da shirin shugaba Salva Kiir, na kiran taron tattaunawar 'yan kasa, yana mai fatan hakan zai baiwa sassan Sudan ta kudun damar warware sabanin dake tsakanin su, da sake nazarta, da bunkasa hanyoyin sulhu cikin hadin gwiwa. Hakan a cewar sa zai haifar da wanzuwar zaman lafiya, da daidaito, da ci gaba a wannan kasa da ke shan fama da tashe tashen hankula.(Saminu Alhassan)