Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang, ya bayyana a nan birnin Beijing cewa, halin da ake ciki a zirin Koriya ya jawo hankali matuka. Kuma kasar Sin na adawa da dukkan wasu kalamai da matakan dake dagula yanayin da ake ciki a yankin.
Kwanakin baya ne mataimakin ministan harkokin wajen kasar Koriya ta Arewa Han Song-ryol, ya ce kasarsa za ta yi karin gwaje-gwajen makamai masu linzami a ko wane mako, da ko wane wata, kuma a ko wace shekara. (Tasallah Yuan)