A yau Talata ne aka gudanar da taron manema labaru, dangane da taron dandalin koli na hadin gwiwar kasa da kasa kan "ziri daya da hanya daya" a nan Beijing.
A yayin taron, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya ce, ya zuwa yanzu shugabanni na kasashe 28 sun tabbatar da cewa, za su halarci taron.
Taron dandalin ya hada da bikin budewa, da taron shugabanni, da taron manyan jami'ai.
Za a bude taron ne da safiyar ranar 14 ga watan Mayu, inda shugaba Xi Jinping na kasar Sin zai halarci bikin, shi ne kuma zai shugabanci taron. (Tasallah Yuan)