in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta kira taron dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar kasa da kasa da shirin "ziri daya da hanya daya" ya shafa
2017-04-16 11:20:55 cri

Za a kira taron dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar kasa da kasa da shirin "ziri daya da hanya daya" ya shafa a ranakun 14 da 15 ga watan Mayun bana a birnin Beijing na kasar Sin.

Taken dandalin tattaunawar shi ne "inganta hadin gwiwa tsakanin kasashe, don raya shirin 'ziri daya da hanya daya', a kokarin samun nasara da ci gaba na bai daya."

A yayin taron, ana sa ran tattaunawa kan yadda za a raya muhimman ababen more rayuwa na kasashen da abin ya shafa, da hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya, da zuba jari kan masana'antu, da raya makamashi, da goyon bayan juna ta fuskar hada-hadar kudi, da cudanyar al'adu, da kiyaye muhallin halittu, da ma hadin gwiwa ta fuskar teku.

A ranar 8 ga watan Maris na bana ne, Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya bayyana cewa, bisa kididdigar da aka yi, kawo yanzu, taron zai samu halartar shugabannin kasashe fiye da 20, da shugabannin kungiyoyin kasashen duniya fiye da 50, da ministocin kasashe fiye da 100, da ma baki fiye da 1200 daga kasashe da yankuna daban daban na duniya.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China