Tsara shirin "ziri daya da hanya daya" cikin hadin gwiwa ya dace da halin da kasashen duniya ke ciki yanzu, wato bunkasar kasashen duniya, da dunkulewar duniya baki daya ta fuskar tattalin arziki, da bunkasar al'adu, da kuma ingantuwar hanyoyin sadarwa na zamani.
Sabda haka, an tsara shirin domin raya tattalin arziki yadda ya kamata, da yin amfani da albarkatun kasa da kasa da kuma zurfafa hadin gwiwar kasuwannin duniya, ta yadda za a inganta hadin gwiwar kasashen dake kan hanyar siliki a fannin kyautata manufofin tattalin arziki.
Babban burin tsara shirin "ziri daya da hanya daya" cikin hadin gwiwa shi ne, kara musaya tsakanin nahiyoyin Turai, Asiya da Afirka da kuma yankunan tekun da abin ya shafa, da kara kullawa da kuma karfafa huldar abokantaka tsakaninsu, ta yadda, za a ba da taimako ga kasashen dake kan hanyar siliki wajen cimma burin samun daidaito da kuma neman dauwamammen ci gaba.
Karfafa mu'amalar dake tsakanin kasa da kasa kan shirin "ziri daya da hanya daya" zai inganta shawarwarin dake tsakanin kasashen da abin ya shafa kan manufofin samun ci gaba, ta yadda za a taimakawa juna yadda ya kamata, da raya harkokin zuba jari da cinikayya tare da samar da karin guraben ayyukan yi a kasashen.
Bugu da kari, za a ci gaba da karfafa musayar al'adu tsakanin al'ummomin kasashen, inda za su rika fahimta da girmama juna, tare da shimfida rayuwa mai wadata da kuma zaman lafiya a wadannan kasashe baki daya. (Maryam)