karon farko ke nan da wata kafar watsa labarai ta kaddamar da jarida ta musamman game da dandalin tattaunawar .
Shugaban jaridar El Pais, ya ce ya yi farin ciki da jaridar ta kasance kafa ta farko wajen kaddamar da jarida ta musamman kan dandalin tattaunawar, ya na mai cewa wannan alama ce dake nuna cewa, bangarori daban-daban na kasar Equatorial Guinea, sun amince sosai da manufofin kasar Sin.
Jakadan Sin dake kasar Chen Guoyou, ya ba da sharhi tare da sa sunansa a jaridar ta musamman, inda ya ce kasar Sin na maraba da kasashen Afirka, ciki har da Guinea Ecuatorial da su shiga shirin "Ziri daya da hanya daya", don amfana da nasarorin da za a samu. (Bilkisu)