Hanyar siliki ta gargajiya, hanya ce da marigayi Zhang Qian ya bude, a lokacin da ya kai ziyara sassan yammacin Asiya a matsayin manzon musamman na daular Xihan, kimanin shekarar 139 kafin haihuwar Annabi Isa Alaihissalam.
Hanyar ta fara daga birnin Xi'an na kasar Sin, sa'an nan ta ratsa lardunan Gansu da Xinjiang har zuwa tsakiyar Asiya da yammacinta, hanyar da kuma ta hada kasashen bakin ruwan Bahar Rum.
Saboda yadda aka fi bin hanyar wajen fataucin siliki na kasar Sin, shi ya sa aka rada mata sunan hanyar siliki. Don ko a shekarar 1877, masanin ilmin labarin kasa na kasar Jamus Ferdinand Paul Wilhelm Richthofen a littafinsa mai taken "kasar Sin", ya sanya wa hanyar da ake bi don yin cinikin siliki a tsakanin kasar Sin da kasashen tsakiyar Asiya da kuma Indiya, daga shekarar 114 kafin haihuwar Annabi Isa Alaihissalam zuwa shekarar 127 'hanyar siliki'.
Sai kuma hanyar siliki a kan ruwa, wadda ita ce hanyar da ake bi ta teku a zamanin gargajiya domin gudanar da mu'amalar cinikayya da al'adu tsakanin kasar Sin da sauran sassan duniya, hanyar ta fara ne daga mashigin tekun kudu maso gabashin kasar Sin, ta ratsa zirin IndoChina da sauran kasashen tekun kudancin kasar Sin da kuma tekun Indiya, har zuwa Bahar Maliya da gabashin Afirka da kuma Turai. Hanyar ta kasance hanyar ciniki da cudanyar al'adu a tsakanin Sin da kasashen ketare a kan teku, wadda kuma ta inganta ci gaban kasashen da ta ratsa.(Lubabatu)