Kasa da kasa da suke bin tsarin "ziri daya da hanya daya" suna da bambancin albarkatu, wadanda suke bukatar juna a fannonin da suke da fifiko, don haka ya kamata su kara yin hadin gwiwa a fannoni dake kasa:
Na farko, kara yin hadin gwiwa yayin da ake tsara manufofi. Kara yin mu'amala yayin da ake tsara manufofi zai tabbatar da aiwatar da shirin "ziri daya da hanya daya". Inda ya kamata a kara yin hadin gwiwa a tsakanin gwamnatocin kasa da kasa, da kafa tsarin mu'amala a tsakanin gwamnatocin kasa da kasa.
Na biyu, su yi hadin gwiwa kan gina ayyukan more rayuwa. Fannin hadin kan gina ayyukan more rayuwa shi ma muhimmin fannin ne da aka fi maida hankali yayin da ake aiwatar da shirin. Bisa tushen girmama ikon mallaka, da tsaron kasashen da abin ya shafa, ya kamata kasashen dake bin "ziri daya da hanya daya" su kara yin hadin gwiwa a fannonin tsara shirin gina ayyukan more rayuwa, da tsarin ma'aunin fasahohi, don sa kaimi ga raya irin wannan muhimmiyar hanya a duniya.
Na uku, su yi ciniki cikin sauki. Hadin gwiwar zuba jari da yin ciniki shi ne muhimmin aiki na aiwatar da shirin. Ya kamata a maida muhimmanci kan warware matsalolin samar da sauki ga fannin zuba jari da yin ciniki, da kawar da kariya da akan bayar a fannonin, don samar da kyakkyawan yanayin yin ciniki a tsakanin kasa da kasa a yankin.
Na hudu, su yi hadin gwiwa a fannin kudi. Hadin gwiwar kudi shi ne tabbaci yayin da ake aiwatar da shirin. Ya kamata a zurfafa hadin gwiwa a fannin kudi, don sa kaimi ga kafa tsarin kula da kudaden nahiyar Asiya. Tsarin zuba jari da tattara kudi da kuma tsarin lamuni.
Na biyar, su yi mu'amala a tsakanin jama'a. Mu'amalar dake tsakanin jama'a ita ce tushen zamantakewar al'umma, yayin da ake aiwatar da shirin. Ya kamata a kara mu'amalar al'adu, da ilmi, da kwararru, da kafofin watsa labaru, da matasa, da mata, da kuma bada hidimar sa kai da dai sauransu. (Zainab)