Zirin nan na hade da yankin tattalin arziki na Asiya da Pasific a gabas, tare kuma da yankin tattalin arzikin Turai a yamma, inda aka mai da shi hanyar tattalin arziki mafi tsayi, kuma mafi samun kyakkyawar makoma a duniya.
A watan Oktoban wannan shekara ne kuma, shugaba Xi Jinping ya kai ziyara kungiyar kasashen kudu maso gabashin Asiya ASEAN, inda ya gabatar da raya "Hanyar siliki a teku a karni na 21", wadda ta hade hanyar siliki da ta kasashen kungiyar ASEAN, da ta kasance ginshiki na inganta ci gaban yankunan da ke dab da cibiyar. An hada kan batutuwan nan biyu har aka haifar da babbar shawarar "Ziri daya da hanya daya".
A cikin shekaru uku da suka gabata, an dauki matakin tsara shirin zuwa na tabbatar da "Ziri daya da hanya daya", inda yake samun ci gaba ta hanyar hadin kai.(Bilkisu)