Yayin taron manema labarai da aka yi bayan ganawar ta jiya, Lavrov ya ce bangarorin uku sun dauki harin da Amurka ta kaiwa sansanin sojin saman Syria ranar 7 ga wannan wata, a matsayin abun da bai cancanta ba, kuma ya sabawa dokokin kasa da kasa da ka'idojin MDD.
Ministocin uku, sun kuma kalubalanci Amurka da kasashe kawayenta, su girmama ikon mallakar kasar Syria, da tabbatar da magance sake faruwar makamancin wancan hari dake kara tsananta halin da ake ciki.
Har ila yau, sun bada shawarar gudanar da binciken kwakwaf, karkashin jagorancin hukumar haramta amfani da makamai masu guba ta duniya, domin bincike kan harin makamai masu guba da aka kai kasar Syria a ranar 4 ga wannan wata.
Lavrov ya ce, bangarorin uku, na son warware rikicin kasar Syria ta hanyar siyasa da diplomasiyya, tare da zaburar da gwamnatin kasar Syria da wakilan kungiyoyi masu adawa da ita, su hau teburin sulhu domin fahimtar juna kamar yadda kuduri mai lamba 2254 na kwamitin sulhu na MDD ya tanada.
Bugu da kari, Sergei Lavrov ya bayyana cewa, kasashen uku za su kara hada hannu wajen yakar ta'addanci da 'yan ta'adda dake kasar Syria, tare da hada kan kasashen duniya domin kafa kawancen yaki da ta'addanci. (Zainab)