in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta bukaci a samar da tsaron kayayyakin more rayuwa na shirin ziri daya da hanya daya
2017-02-14 13:40:43 cri

Kasar Sin ta bukaci hadin gwiwar kasa da kasa domin samar ta tsaron kayayyakin more rayuwa da aka tanada a kasashen dake karkashin shirin ziri daya da hanya daya domin kare su daga fuskantar hare-haren ta'addanci.

Shirin na ziri daya da hanya daya na kasar Sin, ya samar da muhimman kayayyakin more rayuwa ga kasashen dake hadin gwiwa karkashinsa, kuma shiri ne dake tabbatar da hadin kai da kuma cin moriyar juna a tsakanin kasashen, wanda kuma yake bada fifiko wajen inganta batun samar da kayayyakin more rayuwa.

Liu Jieyi, zaunannen wakilin kasar Sin a MDD ya bayyana wa kwamitin sulhun MDD a yayin mahawara game da batun bada kariya ga kayayyakin more rayuwa daga fuskantar barazanar hare-haren ta'addanci.

Mista Liu ya ce, a halin yanzu kasashen duniya dake cikin shirin na ziri daya da hanya daya sun kai 100, ya kara da cewa, kasar Sin ta lashi takobin karfafa hadin gwiwarta da kasashen a fannonin da suka hada samar da bayanan sirri, da auna girman duk wata barazanar tsaro, da yin hadin gwiwar tabbatar da bin dokoki ta hanyar danganta tsakanin kasa da kasa, domin tabbatar da samar da tsaro a tsakanin kasashen, da samar da tsaron kan iyakokin kasa da kasa domin kaucewa fuskantar hare-haren ta'addanci, da samar da ingantaccen tsaro a kasashen dake karkashin shirin na ziri daya da hanya daya.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China