An bude taron dandalin tattaunawa na manyan jami'ai game da neman samun cigaba mai dorewa a fannin hadin gwiwar da ake yi tsakanin kasashe masu tasowa a yau Jumma'a a yankin Hong Kong na kasar Sin. Rahotanni sun bayyana cewa batun "shirin zirin tattalin arziki na siliki da hanyar siliki ta ruwa na karni na 21" wanda kasar Sin ta gabatar, zai zamo daya daga cikin muhimman batutuwa mafiya jawo hankalin mahalarta taron.
Shugaban sashi mai kula da batun yankin Asiya da Pacific na kwamitin neman samun cigaba mai dorewa kan hadin gwiwar da ake yi tsakanin kasashe masu tasowa, mista Cai E'sheng, ya bayyana a gun wani taron manema labaru cewa, "shirin ziri daya da hanya daya" ya dace da "shirin yunkurin neman bunkasuwa bayan shekarar 2015" wanda MDD ta tsara.
A halin yanzu, kasashen duniya daban daban na mai da hankali sosai ga shirin da kasar Sin ta gabatar. Baya ga kasancewar shirin na da buri daya da kwamitin neman samun cigaba mai dorewa kan hadin gwiwar da ake yi tsakanin kasashe masu tasowa, a hannu guda kuma zai samar da yanayi mai kyau ga hadin gwiwar da ake yi a fannoni daban daban.(Lami)