A yayin taron, mataimakin daraktan kwamitin kula da harkokin raya kasa da aiwatar da kwaskwarima na kasar Sin mista He Lifeng, ya bayyana cewa yanzu haka shirin "Ziri daya da hanya daya" na samu bunkasuwa sosai, musamman cikin shekaru uku da fara aiwatar da shi.
Ya ce ya zuwa yanzu akwai kasashe sama da 30 da suka cimma yarjejeniyoyin hadin kai tsakanin gwamnatocin su kan wannan shirin. A waje guda, kasar Sin tana kokarin karfafa hadin kai tare da kasashen dake kan hanyar siliki a fannonin ba da ilmi, da raya al'adu, da aikin jinya, da kiwon lafiya, da kimiyya da dai sauransu. (Bilkisu)