A lokacin da muke gudanar da bukukuwan Aid el-Fitr, ina son bayyana goyon bayana ga al'ummar da ta'addanci ya shafa. Jiya ma, 'yan ta'adda suka kai ma hari kan masallacin manzon Allah Annabi Muhammadu (SAW) ne dake Madina. Suna kai hare hare a ko ina domin janyo mutuwa da tashin hankali, in ji shugaban Senegal.
Mista Sall ya nuna cewa gwamnatin Senegal ta dauki dukkan matakan da suka dace domin yaki da ta'addanci. Yaki da ta'addanci, yaki ne na kowa da kawo. Yaki ne na al'ummar kasa da ya kamata su shiga aikin kare kasarsu ta hanyar bayanai, sadarwa da taimakawa jami'an tsaro, a cewar shugaban Senegal.
Ya kasance a Turai, Amurka, Asiya, Afrika, ko ina wannan rashin imani na janyo mutuwa da tashin hankali. Dole ne, mu bayyana goyon bayan mu da kuma fuskantar wannan annoba, in ji mista Sall.
An dai gudanar da sallar Idin a babban masallancin Dakar, cikin tsaurarrun matakan tsaro daga ciki da wajen wannan gini. (Maman Ada)