in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masar ta tabbatar da asalin mai tashe harin birnin Tanta
2017-04-14 13:52:46 cri
Ma'aikatar harkokin cikin gida ta kasar Masar ta ce, ta tabbatar da asalin wanda ya kai harin kunar bakin wake a birnin Tanta dake arewacin kasar a ranar 9 ga wata.

Sanarwa da ma'aikatar ta fitar a jiya, ta bayyana maharin a matsayin Mahmdouh Ameen Bughdadi, wanda aka haifa a shekarar 1977 a birnin Qena dake kudancin kasar.

Haka kuma, ma'aikatar ta tabbatar da asalin maharin birnin Alexandria, inda ta ce maharan biyu sun fito ne daga birnin Qena, kuma mayaka ne dake bautawa kungiya mai tsattsauran ra'ayi guda.

Sai dai, ma'aikatar ba ta yi karin bayani kan ko kunigyar na da alaka da kungiyar IS ba.

A ranar 9 ga wata ne, aka kai hare-hare bi da bi a birnin Tanta da birnin Alexandria dake arewacin kasar Masar, wadanda suka haddasa mutuwar mutane a kalla 45, yayin da wasu sama da 100 suka jikkata.

Bayan aukuwar hare-haren ne kuma kungiyar IS, ta sanar da daukar alhakin su. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China