in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yan sandan Masar sun gano mutumin da ya kitsa harin cocin Alexandria
2017-04-13 10:33:50 cri
Ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar Masar ta ce ta gano mutumin da ake zargin shine ya shirya harin kunar bakin wake wanda ya kashe kansa a cocin Saint Mark a Alexandria, harin da yayi sanadiyyar hallaka kiristoci 11 da musulmi jami'an 'yan sandan 6 a Lahadin da ta gabata.

A wata sanarwar da aka rabawa manema labarai, ma'aikatar harkokin cikin gidan ta ayyana Mahmoud Hassan Mubarak daga birnin Suez, da cewa shi ne ya kitsa harin.

An haifi mutumun ne a ranar 28, ga watan Satumbar 1986 a Qena na kasar ta Masar, kuma ya taba yin aiki da kamfanin manfetur na kasar.

A ranar Lahadi ne, wasu tagwayen boma bomai suka tashi a cocin dake lardin Gharbiya da lardin Alexandria a arewacin kasar Masar, inda mutane 45 suka mutu, sannan wasu 120 suka samu raunuka.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China