Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da sakon jaje ga takwaran sa na Masar Abdel-Fattah al-Sisi, game da harin ta'addanci da aka kai kan wasu majami'u biyu a kasar ta Masar.
Cikin sako da shugaban na Sin ya gabatar a yau Litinin, ya bayyana matukar alheni bisa rasuwar mutane da dama, yana mai jajantawa shugaban na Masar, da iyalan wadanda suka rasa 'yan uwan su, da ma wadanda suka jikkata.
Shugaba Xi ya ce Sin na adawa da duk wani nau'in aiki na ta'adanci. Kuma kasar sa za ta goyi bayan Masar da al'ummar ta, wajen karfafa tsaron kasa, da wanzar da zaman lafiya, tare da yaki da daukacin ayyukan ta'adanci.(Saminu Alhassan)