in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen duniya sun yi Allah wadai da harin da aka kai majami'un Masar
2017-04-10 11:08:24 cri
Wasu kasashe, ciki har da Amurka, da Faransa, da Kuwait, da Iraki, tare kuma da Paparoma sun la'anci hare-haren da aka kai majami'un Masar. Paparoma ya yi shirin kai ziyara kasar Masar a wannan wata, amma har yanzu bai sanar da cewa ko zai canja jadawalin ziyarartasa ba ko a'a.

An kai wasu hare-haren bom kan majami'u a biranen Tanta da Alexandria dake arewacin kasar Masar a ranar 9 ga wata. Wata majiya daga ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar ta ce, hare-haren sun yi ajalin mutane a kalla 43, tare da raunata wasu sama da dari. Kungiyar IS ta sanar da daukar alhakin kai hare-haren.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China