in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban magatakardan MDD ya yi Allah wadai da harin da aka kai majami'un Masar
2017-04-10 11:06:36 cri
Babban magatakardan MDD Antonio Guterres ya fitar da sanarwa ta bakin kakakinsa, inda ya yi Allah wadai kan hare-haren da aka kai Masar, inda ya nemi a hukunta wadanda suka kaddamar da harin.

An kai wasu hare-haren bom kan majami'u a biranen Tanta da Alexandria dake arewacin kasar Masar a ranar 9 ga wata. Wata majiya daga ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar ta ce, hare-haren sun yi ajalin mutane a kalla 43, tare da raunata wasu sama da dari. Kungiyar IS ta sanar da daukar alhakin kai hare-haren.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China