A ranar Litinin ne majalisar zartarwar kasar Masar ta sanar da kafa dokar ta bacin da misalin karfe 1 na rana, sai dai ta ce dole ne ta bukaci amincewar majalisar dokokin kasar kamar yadda dokar kundin tsarin mulkin kasar ta tanada.
Shugaban kasar Masar Abdel Fattah al-Sisi ya bayyana dokar tabacin ne yayin wani jawabi ta gidan talabijin din kasar bayan harin na ranar Lahadi.
Ya ce an dauki wannan mataki ne domin samar da kariya da tsaron kasar domin gujewa yiwuwar kai karin wasu hare haren.
Cikin wani bayani da ya gabatarwa majalisar wakilan kasar, firaiministan kasar Sherif Ismail, ya bukaci a kara daukar matakan yaki da ta'addanci a kasar ta Masar.
A ranar Lahadin da ta gabata ne, wasu tagwayen boma bomai na yan kunar bakin wake suka kaddamar da hari kan coci biyu dake lardunan Gharbiya da Alexandria a arewacin kasar ta Masar inda suka hallaka mutanet 45 da rauna wasu 120. (Ahmad)