in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rasha ta nemi MDD ta gudanar da bincike kan harin makamai masu guba a Syria
2017-04-12 13:00:49 cri

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya ce Moscow za ta nemi MDD ta yi bincike kan amfani da makamai masu guba a Syria, domin tana sa ran za a sake kai wani sabon hari da makamai masu guba a kasar ta gabas ta tsakiya mai fama da rikici.

Yayin wani taron hadin gwiwa tsakanin shugaba Putin da takwaransa na Italiya Sergio Mattarella, shugaba Putin ya ce za su gabatar da korafi a hukumance ga kotun hukunta manyan laifuka ta duniya dake birnin Hague, yana mai kira ga kasashen duniya su gudanar da binciken tsanaki kan batun tare da daukar matakan da suka dace bisa dogaro da sakamakon binciken. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China