A yayin wata tattaunawar da suka gudanar ta wayar tarho, shugabannin Rasha da Iran sun nuna kin amincewa da matakin da Amurka ta dauka na kaddamar hare-hare a kasar Syria, inda shugabannin suka bayyana matakin da cewa tamkar yin karan tsaye ne ga dokokin kada da kasa.
Shugaba Vladimir Putin na Rasha da takwaransa Hassan Rouhani, na Iran, sun bukaci a gudanar da cikakken bincike bisa adalci game da batun yin amfani da makamai masu guba wajen harin da aka kaddamar a lardin Idlib na kasar Syria a farkon wannan makon.
Sanarwar ta ce shugabannin biyu sun bayyana muhimmancin yin hadin gwiwa wajen daukar matakai na siyasa da na diplomasiyya don kawo karshen rikicin yakin basasar na kasar Syria.
Bugu da kari sanarwar ta yi nuni da cewa, shugabannin biyu sun ce a shirye suke su yi hadin gwiwa wajen yakar ta'addanci da kuma tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin gabas ta tsakiya.(Ahmad Fagam)