in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kaddamar da makarantar da Sin ta gina a Sudan ta Kudu
2017-01-15 13:15:18 cri

Hukumonin gudanarwa a jihar Jubek ta Sudan ta Kudu sun kaddamar da wata sabuwar makarantar sakandare wanda aka gina ta bisa tallafIn gwamnatin kasar Sin.

Sabuwar makarantar tana yankin Gudele, a yammacin babban birnin kasar Juba, wanda gwamnatin Sin ta samar da kudi kimanin dalar Amurka miliyan 8 domin aikin gina makarantu guda biyu a Sudan ta kudun.

Makarantar na da fadin mita 2,200, tana dauke da azuzuwan karatu 16 wadanda za su iya daukar dalibai kimanin 1000, sannan an tanadi na'urar samar da ruwa da lantarki mai amfani da hasken rana na tsawon sa'o'i 24.

Gwamnatin jihar Jubek Augustino Jadalla Wani, ya sanar a jiya Juma'a cewa, sabuwar makarantar za ta taimaka wajen rage cunkoson dalibai a azuzuwa, sannan za ta saukaka wahalhalun da yara ke fuskanta wajen yin tafiya mai nisa domin zuwa makarantun sakandare.

Jami'in ya kuma yabawa irin rawar da kasar Sin ke takawa wajen cigaba da daukar matakan wanzar da zaman lafiya a Sudan ta kudun, ya kara da cewar tallafin da kasar Sin ke bayarwa a sha'anin albarkatun man kasar, da fannin ilmi zai taimakawa matasan kasar wajen samun kyakkyawar makoma a rayuwarsu ta nan gaba.

A nasa bangaren Zhang Yi, jami'i mai kula da harkokin kasuwanci a ofishin jakadancin kasar Sin dake Sudan ta kudun, ya ce kammala wannan aiki, ya nuna a fili irin kyakkyawar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.

A cewar mista Zhang, baya ga aikin gina makarantun, gwamnatin kasar Sin za ta fara aikin bada horo ga malaman makarantu a Sudan ta Kudun.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China