in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan ta Kudu ta ki amincewa a kara tura mata sojojin kiyaye yankunanta
2017-01-12 09:42:13 cri
Kakakin gwamnatin kasar Sudan ta Kudu Michael Makuei Lueth ya bayyana a jiya Laraba cewa, kyautatatuwar tsaro a babban birnin kasar Juba, da sauran yankuan dake kewayensa ne ya sa gwamnatin kasar, ba za ta amince MDD ta tura mata karin sojojin kiyaye yankuna ba.

Bugu da kari, ministan tsaron kasar Kuol Manyang Juuk, ya musanta labarin dake cewa, akwai bukatar girke sojoji domin kiyaye yankunan kasar sabo da rikice-rikicen da take fama da su, inda ya tabbatar da cewa, gwamnatin kasarsa za ta tabbatar da tsaro da zaman lafiyar al'ummominta ita kanta.

A ranar 12 ga watan Agustan shekarar 2016 ne, kwamitin sulhu na MDD ya zartas da kudurin aikewa da rundunar sojin kiyaye yankuna mai kunshe da mutane dubu 4 zuwa kasar Sudan ta Kudu, matakin da ya kara adadin sojojin kiyaye zaman lafiya da MDD ta tura kasar zuwa dubu 17.

Ko da yake gwamnatin kasar Sudan ta Kudu ta bayyana amincewarta kan matakin har sau biyu, cikin watan Satumba da watan Nuwanban shekarar da ta gabata, ya zuwa yanzu, ba a samu wani ci gaba dangane da batun ba. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China