Bayan ganawar, ministan harkokin wajen Sin Mista Wang Yi ya bayyanawa kafofin watsa labarai cewa, wannan shi ne karon farko da shugabannin Sin da Amurka suka gana ido da ido tun bayan darewar Trump kan karagar mulki, inda shugabannin biyu suka yi musayar ra'ayi har na tsawon sa'o'i bakwai, dangane da dangantakar dake tsakanin kasashen biyu da ma sauran muhimman batutuwa da suka shafi duniya.
Shugabannin biyu na ganin cewa, ganawar ta samu dimbin nasarori, kuma ta aza tubali ga ci gaban dangantakarsu, tare da bayyana fannonin da bangarorin biyu za su yi kokarin raya su a nan gaba.(Murtala Zhang)