Shugabannin biyu da suka dauki wannan alkawari a jiya Juma'a, sun kuma amince cewa, ganawar ta su a karon farko, da ya gudana a wajen shakatawa na Mar-a-Lago dake jihar Floridan Amurka, ya haifar da da mai ido.
Yayin tattaunawar cikin kwanaki biyu da suka wuce, Shugaba Xi da Trump, sun yi musayar ra'ayoyi kan muhimman batutuwa da suka shafi kasashe da yankunansu da ma duniya baki daya.
Xi ya kara da cewa, ganawarsa da Shugaban Amurka zai taka muhimmiyar rawa ta fuskar inganta huldar dake tsakaninsu.
Har ila yau, ya ce yayin ganawar, sun kara fahimta da aminta da juna, sannan sun cimma matsaya kan batutuwa da dama tare da kulla kyakkyawar alaka ta aiki. (Fa'iza Mustapha)