Shugaba Xi wanda ke ci gaba da ziyarar aiki a Amurka, ya bayyana hakan ne a jiya Alhamis, yayin liyafar da mai masaukin sa shugaba Donald ya shirya masa. Ya ce shi da shugaba Trump sun tattauna da yammacin jiyan, sun kuma cimma wasu kudurori da dama, game da bunkasa alakar kasashen na su.
Ya kuma kara da cewa, kasahen biyu na fatan daga matsayin dangantakar su a fannoniun zuba jari, da na raya diflomasiyya da fannin tsaro. Sauran sun hada da harkokin shari'a, da na tsaron yanar gizo, da raya al'adu da musaya tsakanin al'ummun kasashen biyu, karkashin manufar mutunta juna da cin gajiya tare.
Shugaban na Sin ya kara da cewa kasashen biyu na kiyaye sabanin dake tsakanin su, tare da kokarin warware batutuwa masu sarkakiya ta hanyoyin da suka dace. Har wa yau shugaba Xi ya bayyana aniyar kasar sa, ta hada kai da Mr. Trump, wajen ciyar da alakar sassan biyu gaba.
Shi kuwa a nasa bangare Mr. Trump taya shugaba Xi murna yayi, bisa jagorantar kasar Sin da ya yi ga samun karin ci gaba, lamarin da ya sanya kimar kasar ta Sin ke karuwa a idon duniya. (Saminu)