A ziyarar aikin ta kwanaki biyu a jihar ta Florida, Xi zai gudanar da wata ganawa da mista Trump a wani masauki na musamman na Mar-a-Lago, wanda ake yiwa lakabi da fadar "White House ta kudanci", inda shugabannin biyu za su tattauna game da huldar dake tsakanin kasashensu, da batun shiyyoyi, dama sauran batutuwan da suka shafi duniya baki daya.
Dama dai tun a ranar 31 ga watan Maris, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Zheng Zeguang, ya shedawa manema labarai cewa, shugaba Xi da mai dakinsa Peng za su halarci wani taron liyafa wanda shugaba Trump da uwar gidansa Melania za su shirya musu.
Zheng ya kara da cewa, a yanayin da duniya ke cikin a halin yanzu, tattaunawar tsakanin manyan shugabannin kasashen biyu abu ne mai matukar muhimmanci da ake sa ran zai karfafa hadin kan dake tsakanin Sin da Amurkar a wannan karni, kana zai kara dankon zumunci da zaman lafiya da kwanciyar hankali, da kuma karfafa tsaro da zaman lumana da samun bunkasuwa a yankin Asiya da tekun Pasific, dama duniya baki daya.(Ahmad Fagam)