A daren jiya Alhamis, shugaban kasar Sin Xi Jinping da uwar gidansa Peng Liyuan suka halarci liyafar maraba wanda takwaransa na Amurka Donald Trump da mai dakinsa Melania Trump suka shirya musu a masauki na musamman na Mar-a-Lago dake lardin Florida.
A yayin liyafar, shugabannin biyu sun gabatar da jawabai daya bayan daya. Shugaba Xi ya ce, shi da shugaba Trump sun yi shawarwari yadda ya kamata, kuma sun cimma ra'ayin bai daya kan bunkasuwar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.
A nasa bangare, shugaba Trump ya bayyana cewa, kasar Sin ta samu babbar nasara wajen bunkasuwarta a karkashin jagorancin shugaba Xi, hakan ya sa Sin tana samun girmama daga kasashen duniya.
Baya ga haka, shugabannin biyu sun yi musayar ra'ayoyinsu kan batutuwan na kasa da kasa da na shiyya-shiyya dake jawo hankulansu baki daya. (Bilkisu)