Yayin ganawar, shugaba Xi Jinping, ya yi nuni da cewa, ya kamata a yi amfani da wani dandali na sada zumunta tsakanin biranen kasashen biyu, domin inganta yin mu'amala da hadin gwiwa tsakanin wurare daban- daban na kasashen, tare da kara yaukaka dankon zumunci tsakanin jama'arsu.
A nata bangare, Lohela ta bayyana cewa, ci gaban da kasar Sin ta samu wata dama ce ga kasar Finland, inda ta yi fatan kasashen biyu za su kara hadin gwiwa a fannonin tattalin arziki da cinikayya da raya al'adu da wasannin lokacin hunturu da harkokin kasa da kasa da sauransu. (Zainab)