Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya bayyana aniyar sa ta saka dan ba, na bunkasa dangantakar kasar sa da Amurka tare da shugaba ta mai ci Donald Trump, ta yadda matsayin alakar kasashen biyu zai kai ga sabon matsayi a tarihi.
Shugaba Xi ya bayyana hakan ne a jiya, yayin ganawar da yayi da Mr. Trump a fadar Mar-a-Lago dake jihar Florida. Ya ce akwai dalilai masu tarin yawa, da za su wajabta ci gaba da raya dangantakar Sin da Amurka, duk kuwa da sabanin dake tsakanin sassan biyu a wasu fannoni.
Shugaban na Sin ya ce tun bayan saisaita dangantakar diflomisyya tsakanin sassan biyu yau shekaru kusan 45, an rika samun ci gaba sannu a hankali, kuma hakan ya samar da alfanu mai tarin yawa ga al'ummun kasashen biyu.
Shugaba Xi ya kara da cewa, kwazon jagororin kasashen ne ya haifar da wadannan nasarori da aka cimma cikin shekaru 45. Daga nan sai ya mika goron gayyata ga shugaba Trump, na ya ziyarci Sin cikin wannan shekara ta 2017.
Da yake maida jawabi, shugaban na Amurka ya amince da goron gayyatar da takwaran sa na Sin ya gabatar masa, yana mai cewa nan ba da jimawa ba zai shirya ziyartar kasar ta Sin.(Saminu)