Liu Jieyi ya ce, daukar matakan soji ba zai kai ga warware rikicin ba, sai dai ma ya kara tsunduma jama'ar Siriya cikin mawuyacin hali, da kara ta'azzarar rikicin kasar gami da kara tashe-tashen hankula a wannan yanki, yana mai cewa, hakan ba zai dace da manyan bukatun al'ummar Siriya da ma sauran kasashen duniya ba.
Liu ya kara da cewa, ana samun bullar wasu sabbin al'amura yayin da ake kokarin yaki da ayyukan ta'addanci a wasu sassan Siriya, inda ya ce kamata ya yi kasashen duniya su yi hattara sosai, tare da murkushe dukkanin kungiyoyin 'yan ta'adda da MDD ta ayyana.
Da sanyin safiyar jiya Juma'a ne, jiragen yakin Amurka suka harba wasu makamai masu linzami guda 59, kan wani sansanin sojan saman gwamnatin Siriya na Shairat dake tsakiya maso yammacin kasar.
Karon farko ke nan da Amurka ta kaddamar da harin kan gwamnatin Siriya bayan darewar Donald Trump kan karagar mulkin kasar.(Murtala Zhang)