in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan wajen kasar Syria ya tabbatar da fashewar wasu makamai masu guba a maboyar makaman 'yan adawa
2017-04-06 19:23:12 cri
Ministan harkokin wajen kasar Syria Walid al-Moallem, ya tabbatar da cewa wasu makamai masu guba dake jibge a maboyar mayakan 'yan adawar kasar sun fashe, yayin da dakarun gwamnatin kasar suka kaddamar da wasu hare hare ta sama.

Walid al-Moallem wanda ya bayyana hakan a Alhamis din nan, yayin wani taron manema labarai, ya ce harin na birnin Khan Sheikhoun ya lalata maboyar makaman da 'yan adawar ke amfani da su, ciki hadda wasu masu guba.

Ya ce duk wasu zarge zarge da ake yiwa sojojin gwamnatin Syria na amfani da makamai masu guba karyace tsagwaron ta. Ministan ya kuma nanata cewa, gwamnatin Syria ba ta da makamai masu guba, balle ma ta yi amfani da su a kan fararen hula.

Rahotanni dai sun tabbatar da mutuwar mutane 70, baya ga wasu da dama da suka jikkata, bayan da suka shaki wani nauyin guba a birnin Khan Sheikhoun dake lardin Idlib na kasar ta Syria. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China