in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rundunar sojin Syria ta musunta yin amfani da iska mai guba a yankin dake karkashin ikon masu adawa da gwamnatin kasar
2017-04-05 11:15:51 cri
Rundunar Sojin Syria ta musunta labarin da ke cewa, wai sojojin gwamnati sun yi amfani da iska mai guba a jihar Idlib dake arewa maso yammacin kasar, da ya kasance karkashin ikon 'yan adawa.

Hukumar kula da hakkin dan Adam ta kasar Syria da cibiyarta ke birnin London na kasar Birtaniya, ta bayyana cewa, an kai harin iska mai gubar ne ta sama, a wani garin dake jihar Idlib a jiya Talata, al'amarin da ya haddasa mutuwar mutane a kalla 58 tare da raunata wasu da dama.

Hukumar dai ba ta bayyana mamallakin jiragen yakin da suka kai harin ba tsakanin sojojin gwamnatin Syria da sojojin Rasha, da kuma na kawancen kasa da kasa da Amurka ke jagoranta dake yaki da kungiyar IS. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China