Rahotanni daga kafofin watsa labaru dai sun tabbatar da mutuwar kusan mutum 70, baya da wasu 200 da suka jikkata, sakamakon shakar iska mai guba da suka yi a ranar Talata, a garin Khan Sheikhoun dake lardin na Idlib.
Game da aukuwar wannan lamari, kakakin ma'ikatar tsaron Rasha Igor Konashenkov, ya fidda wata sanarwa dake cewa, dakarun gwamnatin Syria sun kaddamar da wasu hare hare ta sama, kan maboyar makaman 'yan tawayen kasar dake gabashin Khan Sheikhoun, wanda hakan ya haddasa fashewar makamai masu guda da 'yan adawar suka boye.
A sana bangare kuma, ministan harkokin wajen kasar Syria ya sake jaddada cewa, gwamnatin kasar ba ta da wasu makamai masu guba, balle ma ta yi amfani da su kan fararen hula.
A Larabar nan ne dai ake sa ran kwamitin tsaron MDD, zai yi wani zama na musamman domin tattaunawa game da aukuwar hari da makamai masu guda a kasar ta Syria. (Saminu)