Gwamnatin Syria ta goyi bayan kasa da kasa su yi bincike kan batun makamai masu guba
Mataimakin firaministan kasar Syria kuma ministan harkokin wajen kasar Walid Muallem, ya bayyana a ranar 6 ga wata cewa, kasar Syria tana nuna goyon baya ga kasa da kasa da su kafa kwamitin yin bincike kan batun yin amfani da makamai masu guba a jihar Idlib dake arewa maso yammacin kasar, amma ya kamata a magance yin amfani da kwamitin wajen cimma yunkurin siyasa. A wannan rana kuma, shugaban kasar Rasha Vlładimir Putin da firaministan kasar Isra'ila Benjamin Netanyahu sun buga waya da bayyana cewa, game da batun yin amfani da makamai masu guba a kasar Syria, ba su amince da duk irin zargin da aka yi wa kasashensu kafin a yi bincike kan batun.
A ranar 4 ga wata a jihar Idlib dake kasar Syria, an kai harin makamai masu guba, wanda ya haddasa mutuwa da raunatar mutane da dama, kana ya jawo hankalin kasa da kasa sosai. (Zainab Zhang)